undunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto
mutane 338 daga hannun kungiyar Boko Haram a
kauyuka daban-daban na jihar Borno.
A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar
Sani Usman Kukasheka ya fitar, ya ce mutanen da aka
ceto sun hada da maza takwas da mata 138 da yara 192.
Ya kara da cewa an kai su garin Mubi da ke jihar
Adamawa domin duba lafiyarsu.
Kanar Kukasheka ya ce dakarunsu sun kashe 'yan
kungiyar boko Haram 30, sannan suka lalata manyan
sansanoninsu a kauyuka hudu da ke kusa da dajin
Sambisa.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kwato makamai
daban-daban daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.
Title :
Boko Haram: Sojin Nigeria sun ceto mutane 338
Description : undunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 338 daga hannun kungiyar Boko Haram a kauyuka daban-daban na jihar Borno. A wata s...
Rating :
5