Wasu Malamai mabiya addinin gargajiya a Nijeriya sun ce dodon bautarsu (Ifa) ya gargadi Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Legas, Akinwumi Ambode da su gaggauta yin hadaya ga gumakansu muddin suna son su yi mulki cikin kwanciyar hankali da jin dadi.
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar masu bautar addinin gargajiya ta Nijeriya (AATREN), Cif Ifasegun Elegushi, inda ya ce babban dodon bautarsu (Ifa) ne ya bayar da umurnin hakan a yayin da suka je taron addu’oi na musamman a wajensa.
A cewarsa, da ma sun saba a duk lokacin da suka je bauta, sukan nemi dodon ya ba su bayanai game da halin da Shugabanin kasar nan a matakin tarayya da na jihohi zai kasance da su. Ya ci gaba da bayyana cewa, bayan sun yi bauta, sai dodon nasu mai suna Odus Ifa Oturugbon, ya ba su wahayin cewa, Allolinsu na bukatar hadaya muddin idan ana so Shugaba Buhari da Gwamna Jihar Legas, Ambode su sami nasara a gudanar da mulkinsu.
Kazalika a cewar Bokan, abin bautar nasu ya kuma umurce su da cewa tabbas ana bukatar a yi hadaya ga kasar nan, musamman Jihar Legas domin samun zaman lafiya da ci gaba. Don haka ya roki gwamnatocin kasar nan da su jawo mabiya addinin gargajiya a jiki domin guje wa fushin ababen bautarsu da samun dorewar zaman lafiya da ci gaban dorewar a kasar nan baki daya.