Wata kungiya mai suna Conference of Nigeria Civil Rights Activists (CNCRA) ta bayyana cewa bata ji dadin da aka tabbatar da Abdulrahman Dambazau a matsayin Minista ba. Kungiyar tayi dogaro da kundun tsarin mulki sakon layi na 147 (1-3) wanda ya bayyana cewa dole kowace jiha a samu Minista daga gare ta. Kungiyar ta bayyana cewa zaben Dambazau ya hana ma mutanen Kano damar su. Jaridar The Guardian ta ruwaito.
Bayan taron ta data gudanar a Akure, jihar Ondo. Shugaban kungiyar Ifeanyi Odili yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari daya cika alkawarin da yayi ma mutane cewa zaya yaki rashawa.
“Muna so munyi kira ga shugaban kasa daya tuna cewar shi. Shi na kowa ne, kuma shi bana kowa bane’, wanda ke jini da cewa Shi baya Tare da masu rashawa, Kuma yana tare da talakawa.”
Abdurahman Dambazau dai tsohon shugaban hafsin sojan kasa ne a lokacin Shugaba Yar’adua. Sannan Shi Dacta ne. Yayi bayani Mai gamsarwa ga Majalisar Dattawa, Wanda Hakan ne ya sanya suka tabbatar dashi.