Aston Villa ta raba gari da kociyanta Tim Sherwood, bayan da ya jagoranci kungiyar watanni takwas.
Villa ta kori Sherwood daga aiki bayan da Swansea ta doke ta 2-1 a gasar Premier da suka yi a ranar Asabar a Villa Park.
Kuma doke ta da aka yi shi ne rashin nasara a wasanni shida da aka ci Villa a jere da hakan ya sa take mataki na 19 a kan teburin Premier.
Villa ta nada kociyan karamar kungiyar mai horas da matasa 'yan kasa da shekaru 21 Kevin McDonald a matsayin rikon kwarya.
Sherwood wanda ya je Villa a watan Fabrairu ya kai kungiyar wasan karshe a kofin FA, sai dai kuma wasa daya ya ci daga guda 10 da ya yi a gasar Premier bana.
Title :
Aston Villa ta sallami Tim Sherwood
Description : Aston Villa ta raba gari da kociyanta Tim Sherwood, bayan da ya jagoranci kungiyar watanni takwas. Villa ta kori Sherwood daga aiki bayan d...
Rating :
5