A ranar Laraba ne ake shiga rana ta biyu ta taron da ake
yi a Maiduguri kan yadda za a tallafa wa 'yan gudun
hijira a arewa maso gabashin Najeriya.
Taron ya hada da masu ruwa da tsaki da suka hada da
hukumomin tarraya da na jahohi da kuma kungiyoyi
masu zaman kansu.
Shugaban kwamitin da zai nemi tallafin, Alhaji
Muhammad Sani Zorro, ya ce za a dauki matakai na
ganin cewa agajin da za a bayar ya kai ga wadanda aka
bayar domin su.
Jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriyar na daga
cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.
Sai dai a daidai lokacin da ake wannan taro na tara tallafi
ga 'yan gudun hijirar, wasu 'yan gudun hijirar daga jihar
sun koka da cewa su ba su da sansanoni a cikin jahar.
Title :
Ana taron tallafa wa 'yan hijira a Nigeria
Description : A ranar Laraba ne ake shiga rana ta biyu ta taron da ake yi a Maiduguri kan yadda za a tallafa wa 'yan gudun hijira a arewa maso gabas...
Rating :
5