Yayin da ‘yan Najeriya, ke shagulgulan ranar samun yancin kai na chika shekaru 55, rahotani daga jahar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata cewa ‘yan kungiyar Boko Haram, ne sun farma wani gari a yankin Madagali, da ke iyaka da jahar Borno,
Maharan dai sun yiwa wasu mutane yankan Rago ciki har da mata biyu, da kona gidaje da kuma sace wa mutanen garin abincin su.
Kawo yanzu dai hukumomin tsaro dai a jahar Adamawa basu ce komai ba dangane da afkuwar wannan lamarin domin da wakilin muryar Amurka,ya tuntubin mukaddashin kakakin rundunar Soja ta 23, dake Yola, Kaftin, Ja;afaru Nuhu, yace suna taro amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton bamu ji daga gare shi ba.
Sai dai dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Madagali da Michika, Mr. Adamu Kamali, ya tabbatar da afkuwar lamarin in da yake cewa a halin yanzu jama’ar yankin na cikin kunci da fargaba.
Title :
An Yiwa Wasu Mutane yankan Rago Ciki Har Da Mata
Description : Yayin da ‘yan Najeriya, ke shagulgulan ranar samun yancin kai na chika shekaru 55, rahotani daga jahar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya...
Rating :
5