Kotun daukaka karar zabuka ta soke zaben gwamnan jihar Rivers tare da dakatar da gwamna Nyesom Wike na jam'iyyar PDP daga mukaminsa.
Kotun wacce ta yanke hukuncin karar a Abuja ranar Asabar, ta kuma bayar da umarnin a sake sabon zaben gwamna a jihar.
Kotun ta kuma yanke wannan hukunci ne sakamakon korafin da dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC Mista Dakuku Peterside, ya shigar na cewa bai yarda da sakamakon zaben ba.
Zaben da aka gudanar a jihar ta Rivers a watan Afrilu ya sha suka daga masu sa ido na kasashen waje da na cikin gida saboda tashe-tashen hankulan da aka yi ta samu tsakanin jam'iyyun APC da na PDP.
Title :
An soke zaben gwamnan jihar Rivers
Description : Kotun daukaka karar zabuka ta soke zaben gwamnan jihar Rivers tare da dakatar da gwamna Nyesom Wike na jam'iyyar PDP daga mukaminsa. Ko...
Rating :
5