Sarkin Kano mai martaba, Muhammadu Sanusi II ya sanar da sauke babban Dan margayi Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero, daga mukaminsa na “Ciroman Kano”,
Sanarwar hakan ta fito ne a yammacin yau Laraba daga Galadima Kano, Abbas Sanusi a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano,
Sanarwar ta ce masarautar Kano ta yanke wannan hukunci ne bayan da Sanusi Ado yaki yin mubaya’a ga sabon sarki Muhammadu Sanusi II,
Kazalika Sanarwar tace an sauke, Alhaji Sanusi Ado Bayero daga mukamin Hakimin Gwale da yake rike da shi,
Galadiman ya kara da cewa an nada Alhaji Nasiru Ado Bayero a matsayin sabon “Ciroma Kano.”
HausaTimes
Title :
An sanar da cire ciroman Kano Sanusi tare da nada sabo
Description : Sarkin Kano mai martaba, Muhammadu Sanusi II ya sanar da sauke babban Dan margayi Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero, daga mukaminsa na “...
Rating :
5