Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bada umurnin rufe makarantar Hassan Gwarzo, inda aka yi zargin an yi yunkurin yi wa yara maza fyade.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar shi ne ya bada umurnin rufe makarantar tare da kafa wani kwamiti da zai binciki zargin yi wa yara maza fyade a makarantar.
A ranar Alhamis ne wasu daliban makarantar da iyayensu suka yi zargin cewa wasu daliban na yi wa yaran fyade ko kuma a wasu lokutan yunkurin yi musu fyaden.
Sai dai hukumomin makarantar sun musanta zargin yin fyade a makarantar.
Mai makarantar, Farfesa Ibrahim Ayagi ya ce "Wannan abu bai afku ba. Abin da muka sani shi ne cewar yara uku sun kai kara wajen shugaban makarantar cewa wasu sun taba wandonsu. Daya daga cikinsu ya ce an shafa wandonsa, sannan aka rufe masa baki. A kokarin yin motsi kuma sai ya gurde bayansa."
Farfesa Ayagi ya kara da cewa "Ba a kyale 'yan wasu ajin su shiga wurin kwanan 'yan wasu ajin.Sannan da dare akwai jami'in tsaro a kowanne daki."
Kwalejin Hassan Ibrahim Gwarzo, makarantar sakandare ce mai zaman kanta a birnin Kano wacce ta dade ta na samar da ilimi ga yara.
karanta tsohon labarin ana nan Ana Zargin yi wa yara maza fyade a Kano'
Title :
An rufe makarantar da ake zargin yi wa yara fyade a Kano
Description : Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bada umurnin rufe makarantar Hassan Gwarzo, inda aka yi zargin an yi yunkurin yi wa yara maz...
Rating :
5