Mahukunta a Somalia sun ce an kashe masu tayar da kayar baya na kungiyar al-Shabab su fiye da hamsin a yayin wata gwabzawa da akayi a kusa da kan iyakar kasar da Habasha.
Kwamishinan Gundumar Hudur, Mohammed Moalim, ya shaida wa BBC cewa 'yan kungiyar al-Shabab din sun kai hari ne da asuba a sansanin da sojojin Somalia da na Habasha suke da asuba.
Ya ce nan take sojojin suka mayar musu da martani inda suka kashe 'yan tawayen hamsin suka kuma raunata ashirin da biyar.
Kwamishinan ya kara da cewa an kashe sojojin gwamnati biyar.
Har zuwa yanzu dakarun Habasha da na 'yan kungiyar al-Shabab ba su ce komai ba game da abin da ya faru.
Title :
An Kashe 'Yan Al-shabab Hamsin
Description : Mahukunta a Somalia sun ce an kashe masu tayar da kayar baya na kungiyar al-Shabab su fiye da hamsin a yayin wata gwabzawa da akayi a kusa d...
Rating :
5