Rundunar sojin Nigeria ta yi karin haske a kan sabuwar
runduna ta musamman ta ashirin da tara a garin
Benisheikh da ke jihar Borno.
Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanal Sani
Usman Kukasheka ya ce "Akwai bataliyoyi a karkarkashin
wannan runduna kuma za ta kasance da kayayyakin yaki
domin kawar da Boko Haram."
"Muna samun nasarori a yakin kuma kara yawan
makamai zai ba mu damar ci gaba da samun nasara," in ji
Kukasheka.
Rundunar har wa yau ta jadda matsayinta na cewa babu
wata karamar hukuma ta jihar Borno da ke hannun Boko
Haram.
An ambato gwamnan jihar Borno Kashim Shattima na
cewa akwai kananan hukumomin jihar guda biyu da har
yanzu suke karkashin ikon 'yan kungiyar Boko Haram.
Su ma wasu 'yan jihar Bornon da ke gudun hijira, sun
jaddada cewa bayanan da suke samu sun nuna cewa har
yanzu yankuna da dama da 'yan Boko Haram ke iko da
su a jihar.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da
20,000 tare da raba wasu miliyoyi daga muhallansu.
Title :
An kafa sabuwar runduna a Benisheikh
Description : Rundunar sojin Nigeria ta yi karin haske a kan sabuwar runduna ta musamman ta ashirin da tara a garin Benisheikh da ke jihar Borno. Kakak...
Rating :
5