Tun daga watan Yuli zuwa yanzu jihohin Borno da
Adamawa suke ta fama da hare-haren kunar
bakin wake da suka lakume rayuwa kusan dari
hudu da jikata wasu da yawa.
Yawancin hare-haren da 'yan
Boko Haram suka kai kwanan nan a jihohin Borno
da Adamawa sun aunasu ne kan masallatai.
Harin baya bayan nan da suka kai kan sabon
masallacin Juma'an Jimeta ya hallaka mutane fiye
da talatin. Na Borno da suka kai makonni biyu da
suka wuce mutane fiye da saba'in suka mutu a
masallacin tare da rusheshi.
Sabili da wadandan hare-haren ofishin jakadancin
Amurka dake Abuja ya fitar da wata sanarwa da
ta fito daga kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen
Amurka John Kirby inda yake yiwa jihohin biyu
ta'aziya.
A sanarwar Amurka ta yi tur da hare-haren kunar
bakin wake da aka kai kan masallatan dake Borno
da Adamawa. Sanarwar ta ambato kakakin yana
bayyana alhini tare da mika ta'aziya musamman
ga iyalan wadanda wannan aika-aikar ta rutsa
dasu.
Amurka tace yin anfani da yara kanana
musamman 'yan mata wajen aikasu su yi kunar
bakin wake na nuna irin matakan da kungiyar
Boko Haram ke dauka tana tayar da hankalin
mutanen arewa maso gabashin kasar da ma zirin
tafkin Chadi.
Sanarwar ta kara da cewa Amurka zata cigaba da
marawa gwamnatocin kasashen dake yankin tafkin
Chadi a cigaba da fafatawa da ake yi na kawo
karshen aika aikar 'yan Boko Haram.
Title :
Amurka Ta Aika da Sakon Ta'aziya
ga Jihohin Borno da Adamawa
Description : Tun daga watan Yuli zuwa yanzu jihohin Borno da Adamawa suke ta fama da hare-haren kunar bakin wake da suka lakume rayuwa kusan dari hudu...
Rating :
5