Majalisar dattawan Nigeria ta tantance, sannan kuma ta amince da Rotimi Amaechi da sauran mutane 17 domin shugaba Muhammadu Buhari ya nada su a matsayin ministoci.
Sanatocin sun amince da Mr Amaechi a matsayin minista duk da adawar da 'yan PDP suka nuna, abin da ya sa shugaban marasa rinjaye, Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci 'yan jam'iyyar PDP suka fice daga zauran majalisar.
Daga bisani shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya nemi sauran sanatocin da suka rage, 'yan jam'iyyar APC mai mulki, su kada kuri'a ta murya, kuma a wannan lokacin ne suka amince da nadin Amaechi da sauran ministo 17.
A ranar 15 ga watan Oktoba ne majalisar ta amince da mutane 18 domin shugaba Buhari ya nada su a matsayin ministoci.
Title :
A Karshe An Amince Da Rotimi Amaechi Da Saura Mutane 17 Ama Sayin Ministocin
Description : Majalisar dattawan Nigeria ta tantance, sannan kuma ta amince da Rotimi Amaechi da sauran mutane 17 domin shugaba Muhammadu Buhari ya nada s...
Rating :
5