A Yayin da yake gabatar da kasida a taron tsaro da aka gudanar a Abuja, Manajan Daraktan kamfanin Dr. Ibe Kachikwu, ya ce kamfanin na aiki wajen ganin an fara amfani da jirage marasa matuka wajen sa ido a kan iyakokin kasar ta ruwa kan jiragen ruwa masu shiga da fitar da man fetur daga kasar.
Dr. Kachikwu ya tabbatar da cewa kamfanin zai yi bakin kokarinsa wajen hana munanan ayyukan da ake yi na satar man fetur cikin watanni takwas.
Manajan Daraktan ya kuma kara da cewa kamfanin zai yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro wajen ganin an kare afkuwar fasa bututun mai a kasar.
Ya ce “In har ba a yi maganin wadannan matsaloli ba, to kamfanin NNPC ba zai samu nasara wajen gudanar da ayyukansa yadda ya kamata da kuma farfado da matatun man fetur ba.”