Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun sha alwashin dawo da martabar yankin a wani taro da suka gudanar a kaduna domin tattaunawa matsalolin da suka addabi yankin.
A sanarwar bayan taron wanda shugaban kungiyar Kashim Shettima na jihar Borno ya karanta yace cikin matsalolin da yankin ke fama da su sun hada da ta'addanci da sace-sacen shanu baya ga rashin aikin yi da ya addabi matasa.
Gwamnonin sun kuduri aniyar tunkarar matsalolin ne ta hanyar samar da ayyukan yi da farfado da masana'antu da masaku, musamman masakar nan ta KTL mallakin jihohin wacce ta durkushe a cewarsu
A dunkule dai gwamnonin na arewa na cewa a wannan karo a tsaye suke har sai sun dawo da martabar yankin.
An gudanar da taron na gwamnonin ne a fadar gwamnatin jihar Kaduna a inda gwamnonin jihohin Kaduna da Jigawa da Kano da Borno da Zamfara da Benue da Taraba da Nasarawa da Bauchi suka halarta, jihohin Kogi da Kwara kuwa suka samu wakilcin mataimakan gwamnoninsu.
Title :
Za mu dawo da martabar Arewa - Gwamnoni
Description : Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun sha alwashin dawo da martabar yankin a wani taro da suka gudanar a kaduna domin tattaunawa matsaloli...
Rating :
5