Nijeriya dai za ta cika shekaru 55 ne da samun ‘yanci a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da fitar da naira milyan 70 domin gudanar da shagulgulan bikin zagayowar shekarar samun ‘yancin Nijeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, shi ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Talata, ta bakin sakataren dindindin na ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
Babachir, ya kara da cewa, Buhari ya yi karfin hali wajen fitar da naira milyan 70 ne bayan ya yi korafin cewa maimaikon barnatar da kudin wajen bikin, gara a yi amfani da su wajen biyan albashin ma’aikata.
Title :
Za A Fitar Da Naira Milyan 70 Domin Bikin Zagayowar Shekarar Samun ‘Yancin Nijeriya
Description : Nijeriya dai za ta cika shekaru 55 ne da samun ‘yanci a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa. Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da f...
Rating :
5