Ana sa ran za a cire Nigeria daga cikin jerin kasashen da cutar Polio ta zama annoba, a wani mataki da ake kallo a matsayin "gagarumar nasara" a yaki da cutar.
Ana sa ran hukumar lafiya ta duniya WHO za ta ba da sanarwar hakan a taro kan cutar a birnin New York.
Hakan ya biyo bayan shafe fiye da shekara guda ba tare da an samu bullar cutar ba kasar.
Idan har aka kwashe shekaru uku ba a samu wanda ya kamu da cutar Polio ba a kasar, to za a ayyana kasar a matsayin wacce ta kawar da cutar Polio baki daya.
Abin da hakan ke nufi shi ne, kasashe biyu watau Pakistan da Afghanistan su ne ka dai suka rage a matsayin kasashen da cutar Polio ta zama annoba.
Jean Gough, wakilin Unicef a Nigeria ya ce : "Wannan gagarumar nasara ce. Amma kuma ya yi wuri a soma murna. Sai mun ci gaba da zage damtse domin kawar da Polio baki daya."
Polio na yaduwa sosai a tsakanin kasashe ne sakamakon rashin yin allurar rigakafin cutar.
Cutar Polio na janyo shayewar kafa idan yaro ya kamu da ita.
Title :
Za a cire Nigeria cikin jerin kasashe masu Polio
Description : Ana sa ran za a cire Nigeria daga cikin jerin kasashen da cutar Polio ta zama annoba, a wani mataki da ake kallo a matsayin "gagarumar ...
Rating :
5