Yau da kullum tasa na fahimci cewar akwai Mazaje da yawa wadanda suke tilasta Matayensu SU ZUB DA CIKI bisa dalilansu da son zuciyarsu kala-kala.
Mafiya yawan masu irin wannan ta'addancin an fi samunsu acikin 'Yan Boko. Dama mutum ya riga ya raina albashinsa, yana ganin kamar ba isarsa zai yi ba. Don haka ba yaso ya haifi 'ya'ya ds yawa. Wai kar suzo su cinye masa kudin albashinsa..
Saboda toshewar basira, da ragon azanci da kuma koyi da dabi'un kafirai shi yasa ya manta da cewa Allah ne mai azurtawa, kuma shi keda ikon azurta bawansa idan yaso, ta yadda yaso.
Wasu kuma sun samo cikin nd ta hanyar sharholiyarsu. Don haka dole su zub dashi wai don kar asirinsu ya tonu aduniya... Ko yaya zasuyi kuma aranar Babban tonon silili agaban zatin Ubangiji!!!
- Shin kun tanadi amsar da zaku bama Ubangiji idan ya tsayar daku domin hisabi aranar tashin hankali!??
- Shin Kun tanadi amsar da zaku bama wannan Jaririn idan yazo gabanku domin neman hakkinsa na kusan ransa da kukayi??
- Ko kuna tunanin cewa Ubangiji zai manta da laifin da kuka aikata ne?? ko kuma kuna tsammanin cewa ba zai tashi wannan jaririn bane aranar ALQIYAMAH???
Ya Allah ka kiyayemu daga aikata miyagun laifuka. Aaameeen.