A yau ne al'ummar Musulmi a fadin duniya ke bukukuwan sallar layya.
Bukukuwan dai na zuwa ne kwana guda bayan miliyoyin Musulmin da suka je aikin Hajji suka yi tsayiwar arafa.
Wani muhimmin lamari yayin wadannan bukukuwa na yau shi ne yanka ko layya.
A bisa karantarwar addinin Musulunci, ana layya ne don tunawa da Annabi Ibrahim wanda ya yi yunkurin yanka dansa Annabi Isma'il a matsayin hadaya bayan ya yi mafarkin yin hakan.
Dr Abdulkadir Sulaiman Muhammad, wani malamin addinin Musulunci a Najeria ya ce wanda Allah ya hore wa abin layya, to ya yi saboda Allah ba don ya birge wani be ko ya nuna gazawar wani.
Ya ce wadanda basu samu damar yin layyaba, ba damun kansu za su yi ba, sai dai su roki Allah ya hore musu abin yi nan gaba, sannan kuma a sadar da zumunci.
Title :
Yau Take Sallah
Description : A yau ne al'ummar Musulmi a fadin duniya ke bukukuwan sallar layya. Bukukuwan dai na zuwa ne kwana guda bayan miliyoyin Musulmin da suk...
Rating :
5