Gargadin da 'yansandan suka bayar ya biyo bayan wasu rahotannin siri da suka samu ne cewa akwai yunkurin kai hare haren kunar bakin wake lokacin bikin sallah a jihar
Harin ka iya faruwa wajejen da mutane ke taruwa ko kuma a wuraren ibada musamman a lokacin da ake shirye-shiryen bikin sllah.
Ckin 'yan kwanakin nan 'yan kunar bakin wake na fakewa da jama'a ko wurin ibada su kai hari lamarin da ya rutsa da mutane da dama.
Saboda haka jami'an tsaro sun gargadi jama'a da su sa ido, su kiyaye da inda suke, su lura da duk wanda basu yadda dashi ba su kai rahoto.
Kakakin 'yansandan na jihar Adamawa yace sun sha fadakar da al'umma akan su guji inda zasu dagawa mutane hankali. Kada kuma su rike jaka ko wata leda saboda kada hankalin mutane ya tashi.
Wata matsala kuma ita ce ta rashin kudi. Ma'aikata zasu yi binkin ne cikin babu. Gwamnatin jihar ta roki jama'a da su yi hakuri yayinda take jiran tallafi daga gwamnatin tarayya.
Title :
Yansandan Adamawa Ta Gargadi Jama'a Su Kiyaye Lokacin Bikin Sallah
Description : Gargadin da 'yansandan suka bayar ya biyo bayan wasu rahotannin siri da suka samu ne cewa akwai yunkurin kai hare haren kunar bakin wake...
Rating :
5