Mutane da yawa suna tambayata
da kirana awaya cewar tayaya zasu
hada wayansu tecno android da
computer, amatsayin modem suyi
browsing da ita.
Wannan tasa na fito da wasu
hanyoyi guda biyu, wadanda zaka
iya hada ta da computer sune
kamar haka ta Wi-Fi da USB
CABLE.
YADDA ZAKA HADA TECNO
ANDROID DA COMPUTER TA Wi-Fi
hostpot.
Idan kana bukatar hada ta da
computer ta Wi-Fi, saika bi
wadannan matakan na kasa.
1. Kaje Settings > Wireless &
networks > Tethering & portable
hotspot.
2. Saika duba Portable Wi-Fi
hotspot ka bude shi.
3. Bayan wasu yan dakikoki, Wi-Fi
network din zai bayyana akan
wayan daga same.
4. Sannan kaje portable Wi-Fi
hotspot settings > sannan kayi
configure din Wi-Fi hotspot
.
Wato wurin duka ka cike su,
Username da Password.
> Network SSID= Kasa abinda kaga
dama kamar sunanka ko inkiyarka.
> Security==WPA2 SPK
> Password naka ya kasance guda
takwas zuwa sama
5. Idan ka bude shi, yana dauke da
sunan kamfani, saika bashi naka
kasa masa password yadda kana
hadawa zai fara, amma idan ka
bude ka barshi kara zube, ko kuma
baka bude Wi-Fi dimba, to bazaiyi
connect ba, zaita cewa asa
password.
Ka barshi abude karka rufe,
sannan kayi search nasa.