TAMBAYA TA 1729
********************
ASSALAM ALAIKUM WARAHMATULLAH, MALAM,ALLAH YASAKA MAKA DA ALHERI,YA JIKAN MAHAIFA,YA KAREKA DAGA DUKKAN SHARRI DUNIYA DA LAHIRA.
MALAM DAN GIRMAN ALLAH, DAN DARAJAR ALQUR'ANI KA TAIMAKA MIN DA IRIN ABINDA ALLAH YA HORE MAKA.
DA FARKO NI DALIBI NE A F.C.E.KANO AMMA A KATSINA NAKE.INA FAMA DA MATSALAR OLSA, SANNAN INA JIN WANI ABU YANA TASO MINI AKIRJI ZUCIYATA NAMIN CIWO,INA MAFARKIN WATA MATA NUMFASHINA NA FITA SAMA SAMA. GA RASHIN JIN KARFI. DON ALLAH KA TAIMAKAMIN DA ABINDA ALLAH YA HORE MAKA.NA GODE.BISSALAM.
AMSA
*******
Wa alaikumus Salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Bisa dukkan alamu ita wannan aljanar da kake yaywan mafarkinta ta riga ta shiga Jikinka ne. Watakil hakan ne yasa kake fama da sauran matsalolin dake damunka.
Shawarar da zan baka anan ita ce kayi kokari ka garzayo kazo aduba lafiyarka, Zamu baka magungunan Musulunci wadanda suka dace da larurarka. In sha Allahu muna fatan zaka samu lafiya.
Kafin nan ya kamata ka kula sosai da Sallolimka na farillah, ka yawaita zama da tsarki da alwala. Ka yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah safiya da maraice.
Ka rika yin alwala idan zaka kwanta barci. Kuma ka rika tofa ayoyin tsari kamar si fatiha, Ayatul kursiyyi, Qul Huwallahu, Falaqi da Naasi acikin ruwan zamzam kana sha. In sha Allahu zaka samu sauki da yardar Allah.
Allah ya sawwake.