Yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish mai kafirta musulmi sun kashe sojojin gwamnatin Libiya akalla 7 tare da jikkata wasu 4 na daban a kusa da garin Benghazi da ke gabashin kasar Libiya.
Majiyar rundunar sojin gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da halaccinta ta sanar da cewa: Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Libiya da ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish mai kafirta musulmi ya lashe rayukan sojojin Libiya akalla bakwai tare da jikkata wasu hudu na daban a kusa da garin Benghazi da ke gabashin kasar.
Majiyar ta kara da cewar ‘yan ta’addan na Da’ish sun kai hari ne kan garin Annawaghiya da ke kudu maso yammacin garin Benghazi da nufin kwace wasu tankokin yaki.
Title :
Yan Kungiyar Ta'addanci Ta Da'ish Sun Kashe Sojojin Gwamnatin Libiya
Description : Yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish mai kafirta musulmi sun kashe sojojin gwamnatin Libiya akalla 7 tare da jikkata wasu 4 na daban a kusa da ...
Rating :
5