Rundunar ‘Yan Sandan jihar Borno sun
ce wasu ‘yan bindiga da ake zargin
‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai
hari inda suka kasha kimanin mutane
goma a jiya Lahadi a kauyen Mailari
dake karamar Hukumar Konduga.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar
Aderemi Opadukun ya tabbatarwa
manema labarai aukuwar harin inda, ya
bayyana cewa nan take ‘yan Bindigar
suka kashe mutane tara, wasu mutane
10 kuma suka sami raunuka.
Aderemi, ya kara da cewa, dan
tsakanin nan dai mutane akalla 140
suka rasa rayukansu sakamakon hare-
haren da aka samu a Maiduguri da
kuma Mongono a cikin jihar Borno.
Title :
‘Yan Bindiga Sun Kashe
Mutane Tara A Borno
Description : Rundunar ‘Yan Sandan jihar Borno sun ce wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari inda suka kasha kimanin ...
Rating :
5