An yi kira ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gaggauta sauke Gwamnan babban bankin kasar nan, sakamakon rashin sanin tabbas na halin da tattalin arzikin kasa, da kuma yadda hauhawar farashin kayan amfanin al’umma ke neman durkusar da harkokin kasuwanci a fadin kasar nan, wanda hakan ke tabbatar da gazawar Gwaman.
Wannan kira ya fito ne daga bakin Tsohon Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, kuma mai fashin baki kan harkokin tattalin arzikin kasar nan, Alhaji Sunusi Umar Ata [Salo] a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano. Inda kuma ya nuna rashin gamsuwa da salon shugabancin Gwamnan bankin, musamman kan batun rage adadin kudin da mutum zai iya fitarwa ta hanyar ATM, daga N150,000 ya dawo da shi N60,000. Ya ce, yin hakan na nuni da cewa ke nan sai dai ‘yan kasuwa su hakura da kai kudadensu banki, wanda kuma ka iya haifar da babbar matsalar yawaitar fashi da makami.
Da yake karin bayani game da na’urar nan ta cinikayya kuwa, Alhaji Ata cewa ya yi, ai ba kowa ne ya ma san yadda zai yi amfani da ita ba. “Mutun nawa ne suka ma san yadda ake amfani da irin wannan na’ura? Ina tabbatar maka, duk fadin Kantin Kwari, da wiya ka samu POS goma. Kuma ma wasu abokan ciniki na tsoron yin amfani da irin wannan na’ura, sakamakon rashin isasshen wayar da kai da mahukunta suka kasa yi.”
Ya ci gaba da cewa Gwamnan babban bankin, ya rushe asusun amfani da Dala, wanda hakan ya bude kofofin fasa-kaurin Dala zuwa kasashen waje. Ya ce a baya gwamnati na iya sanin adadin Dalolin da ake amfani da su, amma yandu kuwa harkar ta koma ta bayan fage, wanda hakan ya bude wa wasu jami’an tsaro kofar yin hada-hadarsu hankali kwance. Saboda haka tun da wannan Gwamnan ba zai iya ba, Buhari ya gaggauta tsige shi.
Title :
‘Ya Kamata Buhari Ya Tsige Gwamnan Babban Bankin Nijeriya’
Description : An yi kira ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gaggauta sauke Gwamnan babban bankin kasar nan, sakamakon rashin sanin tabbas na halin da t...
Rating :
5