Manzon Allah (saww) ya kasance idan wani bakin ciki ko damuwa ya sameshi yana yin addu'a yana cewa:
"YA HAYYU YA QAYYOUM BIRAHMATIKA ASTAGHEETHU".
(Tirmidhy ne ya ruwaito).
Ya kasance acikin addu'o'insa yana neman tsari daga sharrin Bakin ciki, Kasala, Ragwantaka, Rowa, Wahala, Talauci, Kafirci, da kuma Azabar Qabari da Azabar cikin wuta.
Idan kuma wani abu ya faru wanda ya sanyashi acikin damuwa, yana yawan addu'a yana cewa :
"ALLAHU ALLAHU RABBIY LA SHARIKA LAHU".
(Imam Nisa'iy ne ya ruwaito).
Ya kasance idan har yana tsoron faruwar wani sharri daga wasu mutane, yakan yi addu'a yana cewa :
"ALLAHUMMA INNA NAJ'ALUKA FI NUHURIHIM, WA NA'OODHU BIKA MIN SHURURIHIM"
(Jaami'us Sagheer).
Ya kasance yana yawaita yin addu'a ga kansa yana cewa: "ALLAHUMMA YA MUQALLIBAL QULOOBI, THABBIT QALBEE 'ALA DEENIKA"
Wato "Ya Allah, Ya mai Jujjuya zukata! Tabbatar da Zuciyata abisa addininka".
Sannan yana cewa: "RABBANA ÃTINĀ FID-DUNYA HASANAH, WA FIL AKHIRATI HASANAH, WA QINÃ 'ADHABAN NÃR".
Idan yazo kwanciyar barcinsa, yakan karanta Qul-Huwallahu da Falaqi da Nasi Qafa uku uku ya tofa ahannayensa ya shafe dukkan jikinsa. Kuma yakan yi sauran addu'o'in barcinsa.
Idan ya kwanta kuma yakan dora gefen fuskarsa na dama abisa tafin hannunsa sannan yayi addu'a yana cewa:
"ALLAHUMMA QINEE ADHABAKA YAUMA TAB'ATHU 'IBADAKA''
Wato "Ya Allah ka kiyayeni daga azabarka aranar da kake tashin bayinka".
DAGA ZAUREN FIQHU :
Ya Allah yi salati da tasleemi ga Ma'aikinka sau adadin dukkan halittunka acikin kowanne gwargwadon Qiftawar ido.