Kwallaye 644 aka zazzaga a raga a
gasar Firimiya ta Nijeriya, bayan da aka
buga wasannin mako na 30 a ranar
Lahadi.
Jumullar kungiyoyi 20 na gasar sun
fafata a tsakaninsu sau 300, Kuma dan
wasan Nasarawa United Esosa
Igbinoba, shi ne kan gaba a yawan cin
kwallaye, a inda ya zura 14 a raga.
Tunde Adeniji na Sunshine Stars shi ne
a mataki na biyu a wanda ya ci
kwallaye 13, sai Bright Ejike na
Heartland wanda ya zura kwallaye 12 a
raga.
‘Yan wasa uku ne suka zura kwallaye
goma-goma a gasar da suka hada da
Gbolahan Salami na Warri Wolbes da
Chisom Chikatara na Abia Warriors da
Anthony Okpotu na Lobi Stars da kuma
dan wasan Wikki Tourist Mubarak
Umar.
Sauran wasanni takwas a kammala
gasar bana, kuma za a ci gaba da
wasannin mako na 31 a ranar Lahadi 27
ga watan Satumba.
Title :
WASANNI: An Zura Kwallaye
644 A Gasar Firimiyar Nijeriya
Description : Kwallaye 644 aka zazzaga a raga a gasar Firimiya ta Nijeriya, bayan da aka buga wasannin mako na 30 a ranar Lahadi. Jumullar kungiyoyi 2...
Rating :
5