Assalamu alaikum mallam, dafatan kana lafiya. Don Allah Mallam ga tambayana idan wankan janaba ya kama mutum sai yaje yayi wanka da soso da sabulu kuma baiyi niyyan wankan janaba ba. shin janaban ya fita neh ko yana nan mallam? Ka huta lafiya. Nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Shi wankan Janabah kamar kowacce ibadah, yana bukatuwa zuwa ga NIYYAH. Ita niyyah Farillah ce acikin aikin ibadah irin wannan. Kaga kenan tunda bakayi niyyah ba, to wankan bai yiwu ba. Sai ka sake.
Saboda hadisin Manzon Allah (saww) wanda yake cewa : "AYYUKA SUNA TABBATA NE DA NIYYAH".
Sannan kuma koda kayi niyyar, Dole ne kayi amfani da ruwa mai tsarkin tsarkakewa. Wato ruwan da wani abu dabam wands ba ya tare dashi bai batashi ba.. Don haka wankan soso da sabulu ba ya dauke janabah.
Da fatan Za'a kula.
WALLAHU A'ALAM.