Sallar nan ta bana ta bambanta da dukkan Sallolin Eidi a Tarihin Musulunci. Ba don komai ba, sai don yawaitar rayukan Musulmai Mahajjata wadanda aka rasa alokacin da suke gudanar da ayyukan ibadah a Qasa mai tsarki. Na tabbata kusan dukkan Daliban ZAUREN FIQHU suna da cikakkrn labari akan abubuwan da suka afku.
Sannan mu da muke zaune a gida, mafiya yawan al'ummah sun gudanar da bukukuwan Sallar nan ne acikin QUNCI da rashin Sukuni.
Shin yaya bikin Sallar ya gudana ayankinku, ko Qaramar hukumarku ko Garuruwanku??