Tottenham ta doke Manchester City da ci 4-1 a gasar
Premier wasan mako na bakwai a ranar Asabar.
City ce ta fara zura kwallo ta hannun sabon dan kwallon
da ta sayo a bana Kevin de Bruyne, sai Eric Dier ya
farkewa Tottenham kwallon daga bugun yadi na 25.
Daga nan ne Toby Alderweireld ya ci wa Tottenham
kwallo ta biyu, sai Kane ya kara ta uku kuma kwallon
farko da ya ci wa kulob din a kakar bana.
Erik Lamela ne ya kara cin kwallo ta hudu a ragar City
saura minti 11 a tashi daga karawar.
Wannan shi ne karo na biyu da City ta yi rashin nasara a
gasar Premier, yayin da West Ham ta fara doke ta 2-1 a
Ettihad a makon jiya.
Title :
Tottenham ta ci Manchester City 4-1
Description : Tottenham ta doke Manchester City da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na bakwai a ranar Asabar. City ce ta fara zura kwallo ta hannun s...
Rating :
5