Wasu tagwaye a kasar Kanada, wadanda suke manne ta ka sun ce ba su taba ganin fuskar junansu ba bayan shafe shekara bakwai a duniya, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito ranar Talatar da ta gabata.
A lokacin da aka haifi tagwayen masu suna, Tatiana da Krista Hogan, likitoci sun bayyana wa iyayensu cewa ba za su yi kwana guda ba a duniya, amma sabanin ikirarin da likitocin suka yi, a bana tagwayen suka cika shekara bakwai da haihuwa.
Kamar yadda mahaifiyarsu ta bayyana cewa ’yan matan suna da sha’awar zuwa makaranta da kuma kallon talabijin. Har ila yau, ta ce a kodayaushe sukan kasance cikin annashuwa.
“A lokacin da nake dauke da cikinsu likitoci sun shaida mini cewa abin da zan haifa ba za su samu kyakkyawar rayuwa ba, amma sai na ki amincewa da shawarar da suka ba ni cewa in zubar da cikin. Abin mamaki ma shi ne yadda suke daure wa likitoci kai musamman ta fuskar yadda suke amfani da kwakwalwa guda daya tilo, hakan ya sanya tunaninsu iri guda ne a kodayaushe” inji ta.
Kodayake, likitoci sun ce ba za a iya raba su ba. Amma an ruwaito cewa akwai lokutan da suke fuskantar rashin jituwa a tsakaninsu.