Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta kashe mutane 11 da ake zargin barayin shanu ne a wasu jihohin arewacin kasar.
Sojojin sun ce sun yi nasarar ce a wata arangama da suka yi da barayin a jihar Katsina da sauran jihohin da ke arewa maso yammacin kasar tun daga watan Yuli.
Sojojin sun kuma ce sun kama wasu 'yan bindiga kimanin 64 a lokacin da suke samame a jihohin, sun kuma suka mika su ga 'yan sanda.
Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, kanal Sani Usman Kuka-Sheka, ya ce sun kai samame ne, bayan da gwamnonin yankin su ka nemi dauki daga rundunar sojin domin magance matsalar satar shanu.
Kanal Kuka-Sheka ya kara da cewa daga wannan lokaci zuwa yanzu, an kwato shanu dubu bakwai da dari da 19, da kuma tumaki da awaki da dama.
A cikin 'yan shekarunann dai makiyaya musamman a arewacin Nigeria sun fuskanci babban kalubale daga barayin shanu amma bisa dukkan alamu a yanzu dai jami'an tsaro sun soma gano bakin zaren.