Rundunar sojin Najeriya ta kwace ikon garin Gomboru Ngala, da ke jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram a ranar Talata.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, mai magana da yawun rundunar Kanal Sani Usman KUka-Sheka ya ce yanzu haka dakarun suna ta kokarin tattaro kayan aikinsu da kuma motocin sintiri.
Dakarun sojin Najeriyar na cikin murnar wannan galaba da suka samu a kan Boko Haram.
A baya sojojin Chadi sun karbo garin a hannun 'yan Boko Haram, amma daga bisani kuma suka sake karbe wa.
Title :
Sojin Nigeria sun kwato Gomboru Ngala
Description : Rundunar sojin Najeriya ta kwace ikon garin Gomboru Ngala, da ke jihar Borno daga hannun mayakan Boko Haram a ranar Talata. A wata sanarwa ...
Rating :
5