Na'am Lallai hakika Anso mata suje wajen Sallar eeidi. Babu bambanci atsakanin Tsohuwar mace da yarinya ko matashiya.
Amma bisa sharadin cewa idan fitar da zatayi ba zai janyo fitina gareta ko ga waninta ba.
Amma idan wani zai iya fitinuwa da kallonta idan ta fita, to mafi alkhairi gareta shine ta zauna agidanta.
Hakanan duk matar da take TAKABA, to bai halatta gareta ta fita Masallacin eedi ba. Domin hukuncinta shine ta zauna tayi takabar Wata hudu da kwana goma. Kuma ba zata fito waje ba, sai dai in akwai larurar jinya, ko makamancin hakan.
Ummu 'Atiyyah tace: "Manzon Allah (saww) ya umurcemu mu fito dasu (mata) a sallar eedin Qaramar Sallah, da Sallar Eedin Layya. Da Qananan 'yan mata da masu haila. Har da manyan 'yan mata wadanda ake boyesu agida".
"Amma masu Haila, sai su kaurace ma Wajen Sallar. Amma zasu shaidar da wannan alkhairin da kuma addu'ar Musulmai".
Sai nace: "Ya Rasulallahi wata daga cikinmu bata da Mayafi".
Sai yace: "YAR UWARTA TA SUTURTA-TA DAGA NATA MAYAFIN".
(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Awata ruwayar daga Imamu Muslim da Abu Dawud, Manzon Allah (saww) yace:
"MASU HAILA SU KASANCE ABAYAN MUTANE, SU RIKA YIN KABBARA TARE DA MUTANE".
Anan zamu tsaya, ayi sallah lafiya. Daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (2).