Sarki Salman bin Abdulaziz Al’ Saud na kasar Saudiya ya bukaci hukumomin gwamnatin kasar da su kawar da kalubalolin tsaro dake shafar aikin hajji, domin hana sake aubkuwar irin hadarin daya faru jiyya a Minaa. Sarkin ya bayyana haka ne a yayin da ya gana da shugabannin rundunar tsaron kasar, inda ya bayyana bacin ransa dangane da hadarin da ya auku. Kazalika Sarkin ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan hadari yadda ya kamata, da kuma sanar da sakamakon bincike ga jama'a cikin sauri. Wannan dai shi ne hadari mafi muni a aikin hajji na baya bayan, tun wani makamacin sa daya auku a shekara 2006.
Hausa Radio Tehran
Title :
Saudiyya : Sarki Salman Ya Bukaci A Gaggauta Binciken Abunda Ya Faru Ga Mahajjata
Description : Sarki Salman bin Abdulaziz Al’ Saud na kasar Saudiya ya bukaci hukumomin gwamnatin kasar da su kawar da kalubalolin tsaro dake shafar aikin ...
Rating :
5