Mutane fiye da dari uku ne Allah yayi wa cikawa a wani tirmutsitsi da aka samu a Mina a lokacin aikin Hajji.
Wasu daruruwan kuma sun samu raunika. Jami'ain Saudiyya sun ce al'amarin ya faru ne a Mina, a inda ake jifan shaidan.
Wakiliyar sashen Hausa na BBC, Tchima Illa Issoufou, ta bayyana cewa al'amarin ya rutsa da yan kasar Jamhuriyar Niger da dama.
Kawo yanzu babu takamaiman adadin yan Niger din da abun ya shafa.
A shekarun baya, an yi sha fuskantar turmutsitsi a wajen jifan shaidan, amma bayan wasu gyare gyare da mahukuntan saudiyya suka yi an samu sauki a yan shekarun nan.
Mutane fiye da miliyan biyu ne daga sassa daban daban na duniya suke halartar aikin hajjin na bana.
A farkon aikin hajjin na bana an fuskanci wani mummunan hatsari a lokacin da wata kugiya ta fadawa jama'a a Ka'aba inda mutane fiye da dari suka mutu.
Title :
Sama Da Mutane 300 sun rasu a aikin Hajji Yau
Description : Mutane fiye da dari uku ne Allah yayi wa cikawa a wani tirmutsitsi da aka samu a Mina a lokacin aikin Hajji. Wasu daruruwan kuma sun samu r...
Rating :
5