Rundunar Sojojin Najeriya ta kira taro inda ta shaidawa jama'a cewa daga ranar ba zata sake amincewa da cin zarafin fararen hula ba da sojojinta ke yi.
A karon farko rundunar sojojin Najeriya ta kira taron ganawa da jama'a da fadakar dasu akan matakan da zata dauka dangane da cin zarafin fararen hula.
Shugaban sasanta dangntaka tsakanin sojoji da fararen hula Birigediya Janar Nicholas Rogers yace yanzu lokacin cin zarafin fararen hula ya wuce. Ya bukace duk wanda yake da korafi kama daga wadanda suke korafin an kamasu ba bisa wani laifi ba ko kuma wasu sojoji sun ci zarafinsu da su kai batun ga duk wata rundunar soja dake kusa ko kuma su buga lambar yawarsa kai tsaye. Lambar kuma ita ce 0803 403 6932.
Duk mai korafi ya buga lambar ya shigar da kukansa kowane lokaci. Korafi kan muzgunawa da yiwa mutum barazana ko duka ko kin kiyayewa da dokokin kasa. Yace lokaci ne yanzu da rundunar ta dukufa wajen maido da martabar aikin soji. Yace dole ne su mutunta fararen hula domin da harajinsu ake biyan sojoji.Bai kamata sojoji su dinga yiwa fararen hula barazana ba.
A sansanin 'yan gudun hijira Alhaji Sa'adu Bello babban jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA a Yola yace yanzu an fara samun sauyi a dangantakarsu da sojoji da sauran jami'an tsaro. Sojojin suna kokarin fadakar da kansu akan 'yancin da 'yan gudun hijira ke dashi. Ya yabawa sojoji bisa ga halayensu a sansaninsu.
Shugabannin al'umma ma sun bayyana farin cikinsu da sabon yunkurin rundunar na dakile zin zarafin fararen hula da aka san sojoji da aikatawa. Alhaji Muhammad Ibrahim Itisis mataimakin shugaban 'yan kasuwan Najeriya dake kula da shiyar arewa yana fatan kwalliya zata biya kudin sabulu. Yace da sojoji sai su dokeka su hanaka kuka. Da mai laifi da mara laifi duk sai su hada su ladaftar.
Title :
Rundunar Sojojin Najeriya Ba Zata Amince da Cin Zarafin Fararen Hula Ba
Description : Rundunar Sojojin Najeriya ta kira taro inda ta shaidawa jama'a cewa daga ranar ba zata sake amincewa da cin zarafin fararen hula ba da s...
Rating :
5