Cristiano Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba a
karawar da Real Madrid ta tashi wasa babu ci tsakaninta
da Malaga a gasar La Liga ranar Asabar.
Ronaldo na bukatar cin kwallaye uku domin dara Raul
wanda ya ci wa Real Madrid kwallaye 323 a matsayin
wanda yafi ci mata kwallaye a raga.
Ronaldo shi ne dan wasan Real Madrid dake kan gaba
wajen ci mata kwallaye a gasar La Liga, a inda ya zura
230 a raga.
Malaga ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili,
bayan da aka bai wa Nordin Amrabat jan kati saboda
ketar da ya yi wa Marcelo.
Title :
Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba
Description : Cristiano Ronaldo ya yi takaici da bai ci kwallo ba a karawar da Real Madrid ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Malaga a gasar La Liga ra...
Rating :
5