Idan baku manta ba, kwanakin baya anan zauren fiqhu mun kawo wasu hadisai wadanda suke bayani akan siffar azabobin da Ubangiji ya tanadar ma mazaunan wutar jahannama.
Yanzu kuma zamuyi takaitaccen bayani tare da kawowa Qarin wasu hadisan da zasuyi bayani akan wasu daga cikin rijiyoyin da suke cikin wutar Jahannama (Allah ya tsaremu daga gareta).
Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace: "KU NEMI TSARIN ALLAH DAGA SHARRIN RIJIYAR BAQIN CIKI".
Sai Sahabbai suka ce "Mecece Rijiyar bakin ciki, Ya Ma'aikin Allah?".
Sai yace: "Wani kwazazzabo ne acikin Jahnnama wanda ita kanta Jahannama din akullum tana neman tsarin Allah daga sharrinsa har sau 400".
"AN TANADAR DA WANNAN (KWAZAZZABON RIJIYAR) NE SABODA QARI'AI (MAHADDATAN ALQUR'ANI) MASU KARANTASHI DOMIN RIYA. HAKIKA MAFIYA SHARRIN QURRA'U SUNE MASU KARANTA ALQUR'ANI SUNA NUNASHI AGABAN AZZALUMAN MASU MULKI".
(Tirmidhiy da Ibnu Maajah ne suka ruwaitoshi).
Wannan hadisin ba Qaramin abin tsoro bane. Musamman ma awannan zamanin da zaka ga Mahaddatan Alqur'ani wato Alarammomi sun mayar da Alqur'ani kamar wani abin sayarwa.
AZZALUMAN SHUGABANNI suna gayyatarsu Walima ne, daurin aure ne, taron murna ne, etc.
Da zarar sunje shikenan sai su dauki Microphone su fara RERA QIRA'AH AGABAN MANYAN BAQI... Kuma mafiya yawan wadannan manyan bakin basu dauki Alqur'ani abakin komai ba.
Bassu wa'aztuwa dashi, Kowa yasan haka. Su kansu Alarammomin suna yin karatun ne don neman ABUN MIYA!!!
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (2).