Mai ba shugaban Nijeriya shawara
akan watsa labarai Mr. Femi Adesina
ya bayyanawa manema labarai cewa,
shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari
zai mikawa majalisar dattawan kasar
sunayen sababbin ministocinsa a ranar
Laraba ta karshen wannan watan na
satumba kamar yadda ya yiwa ‘yan
kasar alkawari.
Adesina, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su
cigaba da hakuri akan alkawarinka da
gwamnati ta yi, Shugaba Buhari
mutum ne mai cika alkawari don haka
zai cika wannan alkawarin da ya yi
akan cewa a cikin wannan watan da
muke ciki zai bayyana sunayen
sababbin ministocinsa ga majalisar
dattawa don tantancesu.
Title :
Ranar Laraba Buhari Zai
Mikawa Majalisar Dattawa
Sunayen Ministocinsa
Description : Mai ba shugaban Nijeriya shawara akan watsa labarai Mr. Femi Adesina ya bayyanawa manema labarai cewa, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari...
Rating :
5