A jiya Alhamis ne wato ranar sallah wani mummunan hatsari ya sake awkawa ga mahajja a mina a lokacinda suke kokarin jifan shaidan
, hatsarin da ya tafi da rayukan mahajjata kimani dubu guda. A nan iran dai an rasa mahajjata kimani 125 a hatsarin na Mina.
Kwanaki 23 kacal da awkuwar hatsarin karfen da ya fadawa mahajjata a kusa da dakin Kaaba ya wanda kashe mutane fiye 100, sai gashi a jiya Alhamis kuma sanadiyyar mummunar gudanarwa na mahukuntan kasar Saudia an sake samun wani hatsari wanda ya cinye rayukan hahajjata kimani dubu gudu a Mina a lokacinda suke kokarin jifan shaidan.
Wasu labarai sun bayyana cewa jami’an tsaro masu kula da hanyoyin shiga da fata a wadan nan wurare ne suka tushe mashiga guda daga cikin hanyoyin shiga wurin jifan shaidan wanda ya kai ga mahajjata suka yi ta fadawa kan juna har aka kai ga asarar rayukan mahajjata masu yawa irin haka.
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Sayyed Aliyul Khamianee ya bayyana cewa mummunan tafiyarwa na mahukuntan kasar Saudia ne ya jawo rasa rayukan mahajjata a garin Mina a jiya Alhamis, kuma dole me su dauki alhakin wannan abin bakin cikin da ya faru.
Hatsarin da ya faru a ranar idi a Mina dai shi ne mafi muni irinsa da ya faru a tarihin aikin hajji, sannan wani abin lura a nan shi ne halattar dan sarkin kasar ta Saudia Sarki Muhamman bin Salman bin Abdulazizi da kansa a Mina, tare da jami’an tsaronsa wanda ya kai ga rufe wani ko wasu hanyoyin mahajjata don bashi tsaro, sai kuma wannan rufewar ya jawo takura da cinkosan mahajja wanda ya kaiga abinda ya faru.
Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa dan sarkin ya zo wajen jifan shaitan din ne tare da masu tsaronsa kimanin sojoji 200 da yansanda 150, sannan suka shigo da shi ta hanyar da take akasin inda kwararar mahajjata.
Idan muka dubi irin yadda mahukuntar kasar Saudia suke tafiyar da al-amuran hajja a halin yanzu muna iya cewa sun gaza a cikin wadan nan lamura, don haka ya zama wajibi ga musulmi su nemi bayani mai gamsarwa daga wajen mahukuntan saudia dangane da hatsura guda biyu da suka fadawa musulmi a hajjin wannan shekara, wanda ya hada da faduwar karfen gine gine a kan su ya kashe mutum fiye da 100 sannan ga cinkoson da suka hadasa a Mina wanda ya jawo mutuwar mahajjata daga kasashen duniya daban daban fiye dubu guda.
Title :
[Photos Evidence] Mummunar Tafiya Jami'an Tsaron Kasar Saudia Ne Ya Jawo Mutuwar Mahajjata A Ranar Sallah Ba Yan Afirka
Description : A jiya Alhamis ne wato ranar sallah wani mummunan hatsari ya sake awkawa ga mahajja a mina a lokacinda suke kokarin jifan shaidan , hatsar...
Rating :
5