Paparoma Francis ya kawo babban sauyi wanda ya ba mabiya darikar katolika damar saki su kuma sake aure ba tare da barin cocin ba.
A bara ne Paparoman ya kafa wata hukuma da ta kunshi lauyoyin cocin domin su duba yadda za a yi tsarin sakin mata da sake yin aure, da aka fi sa ni da warwarewa ko 'Annulment' sannan kuma rage kashe kudi.
Idan dai ba a rushe dokar da ta hana sakin da sake aure ba, to yin saki da sake yin auren ka iya zama zina abin da kuma zai haramta wa mabiya katolikan samun kusanci.
Sauye-sauyen dai ba su gurbata koyarwar darikar ta katolika dangane da saki ba.
Masu son su cancanci a basu damar saki ko kuma sake aure, dole ne sai sun tabbatar wa cocin cewar aurensu ba su cika sharudan cocin ba.
Title :
Paparoma ya sauya dokokin aure
Description : Paparo ma Francis ya kawo babban sauyi wanda ya ba mabiya darikar katolika damar saki su kuma sake aure ba tare da barin cocin ba. A bara n...
Rating :
5