Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ware kwanaki
uku daga yau litinin domin juyayin mutuwar ‘yan kasar
22 a turmutsitsin da aka sama ranar alhamis da ta
gabata a lokacin aikin hajji.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya jiyo
Ministan shari’a kuma kakakin gwamnatin kasar Morou
Amadou ya ce, ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu
akwai wasu mutane da dama da suka bata.
A jumulce dai, hukumomin Kasar Saudiya sun tabbatar
da mutuwar Mahajjata 769 cikin kimanin Miliyan 2 da
suka isa Kasar daga sassan duniya domin aikin hajji na
bana, kuma 'Yan Kasar Iran ne hadarin ya fi ritsawa da
su, inda Alhazan Kasar 144 suka rigamu gidan gaskiya.
Sai kuma Kasar Morocco dake biye mata wadda ta rasa
Mahajjatanta 87.
Title :
Nijar ta ware kwanakin juyayin
mutuwar Alhazai
Description : Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ware kwanaki uku daga yau litinin domin juyayin mutuwar ‘yan kasar 22 a turmutsitsin da aka sama ra...
Rating :
5