Tafiya nake ina hada hanya kamar wacce take mayen giya nausawa kawai nake batare da tunanin inda zaniba fatana kawai Allah yakawo abinda zai halakani wata kila zuciyata zata sami saukin zuginda takemiGa radadin da kasana yakemin kamar anyimun matsida barkono tuni hawayena suka kafe saidai tafasar zuciyaYunwa gamida kishirwa suka tilastamin yanke jiki nafadi tuni numfashina yai nisa da gangar jikinaSanyin asuba yatasheni jikina kamar banawaba sabida masifar ciwo haka na yunkura natashi babu motsin komai sai kukan. Tsuntsaye da yacika dajin sam nakasa hade kafafuna sabida ciwo ahaka nacigabada tafiya ina adduar Allah yakawo wanda zaitemakamin tunda lokacin mutuwata baiyibaRana tabude sosai ammabanfasa tafiyaba saide natsaya na huta jinai ana bina amma najuya vanga kowaba sainacigaba da tafiyataSaida karfina ya kare sannan na zauna ina maida numfashi.Sannu baiwar AllahDakyar na amsa dan
wahala yauwa bafulatana me kyawun gaske cikin kayan saki tazauna kusadani ni sunana asma'u wannan yankin mahaifina ke mulkarshi tunfarkon shigowarki wannan daji nake biye dake kuma nasan duk wata damuwarki cikin zafin nama nai kokarin tashi amma nakasa dakyar bakina ya furta karki cutar dani kamar yadda suka sabamin Ni MARAINIYACE.
Humm karki damu bazan taba cutardakeba inaso kidaukeni kamar yar'uwarki kiyi hakuri kinji Allah zaisaka miki ki zauna wajena zantemaki kuma yarima saiyayi dana sanin abinda yai miki kinji da sannu zaki dauki fansaDuk da tsoranta danakeji hakan benani yi mata godiyaba ita tatemakamin harzuwa wata bukka guda daya dake cikin dajin nai wanka tare da tsarkake jikina nai sallah mamaki ya isheni domin cikin bukkar babu abinda babu gashi taimin kashedi da yawan tambaya domin wai tunanina bazai dauki amsarda zata baniba.Wasu magunguna taita bani wai sabida fyaden da akaimin ta karfiTuni na manta da gida munyi wani irin sabo da asma'u cimata takoma na kayan itatuwa kawai suturata bata wuce kayan fulani gabadaya na sauya ammafa dukda haka nakan zubarda hawaye dalilin zalintata da mus'ab yaimin dan sarkin garinmu.Zan iyacwa dagani sai asma'u muke rayuwa adajin saiko dabbobi da tsuntsaye domin tsawan zamana bantaba ganin giccin mutunba akwai tambayoyi masu tarin yawa danakesan yima asma'u amma nakasa domin dana ganta saina manta mezance ahaka na shafe shekara daya muna tare koda yaushe take koyamin karatu na arabic da boko dukda cewa dama nasan wasu abubuwan domin lokacinda nake gida nakusa gama scondry uhmmm zama zai kasance tsakanin jinsin mutun da aljan kuwa?Kubiyoni domin ba afara komaiba
Admin:- Auwal Yusuf Bauchi
Muna Gayyatanku sabon shafin mu danjin maka mantan wannan labarin da ciga banba