Dan kwallon Barcelona, Neymar ya tabbatar da cewar
"sun tattauna" kan batun koma wa Manchester United a
cikin bazara.
Sai dai a cewarsa, United din ba ta nuna da gaske take yi
ba.
Neymar mai shekaru 23 ya ce "Mun tattauna da su,
amma maganar ba ta yi karfi ba."
Tsohon dan kwallon Santos din, ya zura kwallaye 57 tun
lokacin da ya koma Barcelona.
Neymar ya ce zai ci gaba da mayar da hankali a
kwallonsa domin ya zama gwarzon dan kwallon duniya.
Title :
Neymar ya tattauna' da Manchester United
Description : Dan kwallon Barcelona, Neymar ya tabbatar da cewar "sun tattauna" kan batun koma wa Manchester United a cikin bazara. Sai dai a...
Rating :
5