Newcastle United ta buga 2-2 da Chelsea a gasar cin
kofin Premier wasan mako na bakwai da suka yi a St
James Park ranar Asabar.
Newcastle ce ta fara zura kwallaye biyu ta hannun Perez
saura minti uku aje hutu da kuma ta biyu ta hannun
Wijnaldum minti 15 da dawowa daga hutun.
Chelsea ta farke kwallayen da aka ci ta ta hannun
Ramires da kuma Willian wanda ya ci saura minti hudu a
tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Chelsea tana Matsayi na 15 a kan
teburin Premier da maki takwas.
Newcastle United kuwa tana mataki na 19 da maki uku a
kan teburin na Premier.