Da yawa wasu matan (har mazan) suna aikata alfasha koda suna da aure, Hujjarsu ita ce wai sha'awa ce ta damesu. Sun manta cewar Allah be ya halicci rayuwa da dukkan abinda ta Qunsa, domin ya jarrabeka ta hanyar sha'awar domin yaga yadda zakayi.
Shaitan yana iya biyo ma Dan Adam ta hanyoyi da dama, kuma Dan Adam din ya samu nasarar tsallakewa. Amma ba kowanne mutum yake iya tsallake jarrabawa ta fuskar sha'awa ba, sai masu tsananin tsoron Allah.
Kiyi hakuri da Mijinki komai rashin kirkinsa... Duk rashin kirkin Mijinki, ai bai kai fir'auna ba..
Amma ga matar Fir'auna nan ta samu Aljannah tun daga duniya saboda tsananin biyayyarta ga Allah (SWT).
kaima Namiji, kayi hakuri da matarka duk rashin kirkinta ai bata kai Matar Annabi Nuhu ba (as).
Yayi shekaru 950 yana Wa'azi amma duk da haka matarsa ma batayi Imani dashi ba. Hasali ma ita take hana mutane su bada gaskiya dashi.
Amma duk da haka bai saketa ba.. Yaci gaba da zama da ita ahakan, har lokacin da Allah ya gudanar da lamarinsa.
Idan kishiya ko kishiyoyi gareki, to kiyi hakuri kibi Qllah kibi mijinki... Zaki samu nasara.
Kiyi koyi da Nana Aisha Uwar Muminai (ra) ki karanci tarihinta da kyau. Zaki ga yadda ta zauna tare da sauran Matayen Manzon Allah (saww) su Tara, ita ce ta goma. Amma duk da haka bata rage komai acikin soyayyar da takeyi masa ba, sai ma Qarawa takeyi.
Irin yadda take shirya masa girki na Musamman aduk ranakun da yake dakinta. Da kuma yadda take kulawa da kanta wajen ado da kwalliya domin Mijinta (saww).
Idan Mijinki yana sha'awar Qara aure, kar ki hanashi. Domin baki san halin da zaki jefashi ba, idan bai yi auren ba.. Ita ma wacce zai aura din kin hanata samun Miji, kema watarana haka za'ayi ma 'Yarki.
Zaki iya dauke hankalin Mijinki daga kan kowacce mata ta hanyar Nuna masa soyayya fiye da irin ta Budurwa da saurayi...
Kalamai irin na masoya, Wasiku irin na Masoya, Kallo irin na masoya, tarairaya irin ta masoya, Kulawa irin ta masoya, Girki irin na Masoya kwalliya irun ta Masoya, wadannan sune abinda Matan HAUSA FULANI suke zubarwa da zarar sunyi aure sun fara haihuwa. Kuma sune dalilan da Wasu Mazan suke yi musu kishiyoyi acikin gida, ko a waje.
Title :
Nasiha Zuwa Ga Yan'uwa Mata - Part 3
Description : Da yawa wasu matan (har mazan) suna aikata alfasha koda suna da aure, Hujjarsu ita ce wai sha'awa ce ta damesu. Sun manta cewar Allah ...
Rating :
5