Kungiyar Basketball na Najeriya, D’ Tigers ta lashe wasan Basket ball na Afiriki wanda aka gudanar a kasar Tunisia inda ta doke a Angola da 65-74.
Wannan dai shine karo na farko da Najeriya ta dauki wannan ragama. Da farkon wasan dai har kafin a tafi hutu na faro, Angola itace a gaba da 13-10. Amm bayan da aka dawo sai aka canza Olumide Oyedeji da Oguchi bayan da akayi mashi wata keta.
Wasan ya canza inda Najeriya sukayi gumurzu da Angola a 44-37 a zuwa hutu na 2. Amma Angola ta samu rauni inda sukayi ta yin keta.
Wasan Naij.com ya tuna cewa, a 2013 a kada D’ Tigers ne saboda basuyi wani abun kirki ba. Amma kawo wannan Koci dan Amurka Will Voights ya sanya sun yi nasara a wannan karen. Saboda har yanzu sama da kashi 80 yaran ne wadanda suka buga a 2013.
Da aka dawo daga zangon hutu na 3, Angola ta riga ta karaya do in a 36-51 aka tsaya. Dawowa zangon hutu na 4 keda wuya sai D Tigers suka lashe wasan da 56-71.
Dan wasan Najeriya Chamberlain Oguchi yaci lambar girma ta MVP, sannan kuma an bashi ta 3 pointer. Sannan kuma Minnesota Timberwolves da Gorgui Dieng na Sanigal sunci kyauta suma.
Oguchi da Al Farouq Aminu sune suka fi iya bugawa a gare. Najeriya tayi na daya, Angola na Biyun sai kuma masu masaukin baki kuma kasa mai gabatarwa, Tunisia tayi na ukku.
Title :
Najeriya Ta Lashe Wasan Basketball Na Afirika
Description : Kungiyar Basketball na Najeriya, D’ Tigers ta lashe wasan Basket ball na Afiriki wanda aka gudanar a kasar Tunisia inda ta doke a Angola da ...
Rating :
5