Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Inuwa dan’asabe ya ce mutum 66 ne za su amfana da shirin yin kafafun da hannunwan roba ga jama’a inda ya bayyana godiyarsa bisa wannan sabon shiri da uwar kungiyar ta kasa ta bullo da shi a karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Alhaji Inuwa dan’asabe ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Lahadi, inda ya ce matakin da aka dauka na yin hannu da kafafun rofa ga nakasassu ya zo a kan lokaci domin akwai mutane da dama da suke son a yi musu hannayen roba amma ba su da kudin da za su biya saboda talauci da dimbin matsaloli. “Mutum (66) da suka fito daga Jihar Bauchi suka amfana da shirin, kuma sun fito ne daga kananan hukumomin jihar 20 maza da mata,” inji shi.
Ya ce gwamnatin jihar ne ta dauki nauyin kai nakasassun zuwa Abuja.
Daga nan sai ya ce sabon gidan rediyo da kuma talabijin na Manara a kungiyar ta bude kwanakin baya alheri ga Musulmin duniya domin tun lokacin da aka bude rediyon mutane ke addu’o’in alheri ga wadanda suka ba da gudunmawa wajen kafuwarsa.
Alhaji Inuwa ya ce Sheikh Abdullahi Bala mutum ne da kullum bukatarsa addinin Musulunci ya ci gaba.
Ya ce ba Musulmi ne kadai za su amfana da shirye-shiryen gidan rediyon ba har wadanda ba Musulmi a Nahiyar Afirka.
“Addinin Musulunci na bukatar gudunmawar kudi a wannan lokaci domin yanzu makiya suna yakar tunanin matasa ne ta kafofin watsa labarai na zamani wato (Intanet) don haka za mun yi amfani da rediyon Manara wajen wayar da kan al’ummar Musulmi,” inji shi.
Ya ce su a Jihar Bauchi tun lokacin da aka hade bangarorin kungiyar biyu sakamakon rasuwar Alhaji Musa Maigandu ’ya’yan kungiyar suna zaune lafiya kuma suna ci gaba da salloli wuri daya.
Daga karshe ya mika ta’aziyyar kungiyar ga Gwamnan Jihar Barista Mohammed Abubakar da Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da al’ummar jihar dangane da rasuwar Sarkin Misau Alhaji Muhammadu Manga na lll. Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, inda ya ce yana daya daga cikin sarakunan da suke da kima da mutunci a wajen al’umma
Title :
Mutanen Bauchi 66 suka amfana da kafafun roba na Izala
Description : Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Inuwa dan’asabe ya ce mutum 66 ne za su a...
Rating :
5