A yau ne miliyoyin Mahajjata da suka fito daga kasashen duniya daban-daban suka gudanar da hawan Arafa wanda yake a matsayin daya daga cikin rukunan aikin hajji bayan sun kwana a Mina a jiya.
Alhazan dai za su ci gaba da zama a Arafan har zuwa faduwar rana inda za su wuce zuwa Muzdalifa, kana su dawo Mina a safiyar gobe Alhamis inda za su gudanar da jifar Shaidan daga nan kuma su yi Hadaya a gobe Alhamis din don gudanar da bukukuwa ranar babbar salla wadda miliyoyin al’ummar musulmi a duk fadin duniya za su gudanar a gobe Alhamis din.
Rahotanni daga kasar Saudiyyan sun bayyana cewar mahukuntan kasar Saudiyyan sun dau matakan tsaro wajen ganin an gudanar da hawan Arafan lami lafiya. An ce gwamnatin Saudiyyan ta tanadi sama da jami’an tsaro dubu dari don ba da kariya ga mahajjata da aka ce adadinsu ya dara mutane miliyan biyu.
Title :
Miliyoyin Mahajjata Sun Gudanar Da Bikin Hau Arafa A Yau Laraba
Description : A yau ne miliyoyin Mahajjata da suka fito daga kasashen duniya daban-daban suka gudanar da hawan Arafa wanda yake a matsayin daya daga cikin...
Rating :
5